No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Umar Abdullahi Umar, ɗan tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗaya daga cikin manyan daraktocin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban ƙasar ya dakatar da shugaban hukumar, Ahmad Salihijo Ahmad.

Dakatarwar ta sai abin da hali ya yi ta kuma haɗa da wasu manyan daraktoci uku na hukumar kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar ta nuna.

Sanarwar da Mista Ngelale ya fitar a yammacin wannan Alhamis ɗin, ta ce sauran manyan jami’an hukumar uku da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Olaniyi Alaba Netufo da Barka Sajou da Sa’adatu Balgore.

Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan jami’an dangane da zargin karkatar da dukiyar hukumar ta fiye da naira biliyan 1.2 a ɗan tsukukun shekaru biyu da suka gabata.

KU KUMA KARANTA: Ministan Lantarki na Najeriya ya yi barazanar ƙwace lasisin kamfanonin rarraba wuta

Bayanai sun ce hukumomin yaƙi da rashawa sun soma tatso wani kaso daga cikin kuɗin da ake zargin manyan jami’an sun yi ruf da ciki a kai.

Tuni dai shugaban ƙasar ya maye gurbinsu da sabbin shugabanni da suka haɗa da Abba Abubakar Aliyu a matsayin Manajan Darakta na hukumar ta REA.

Sauran waɗanda shugaban ƙasar ya naɗa a matsayin manyan daraktocin da za su maye gurbin waɗanda ya dakatar sun haɗa da Ayoade Gboyega da Umar Abdullahi Umar da Doris Uboh da kuma Olufemi Akinyelure a matsayin shugaban sashen kula da manyan ayyukana hukumar.

Ngelale ya ambato shugaban ƙasar na cewa ana kyautata zaton dukkan waɗanda aka yi wa sabbin naɗin za su sauke nauyin da rataya a wuyansu cikin gaskiya da rikon amana.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...