Wani saurayi mai kimanin shekaru 15 ya kashe ƙanin mahaifiyarsa da wata bindigar farauta ta kakansa a ƙauyen Ogbotobo na ƙaramar hukumar Ekeremor ta Jihar Bayelsa
Lamarin wanda ya faru a ranar Larabar da gabata kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, ya ɗimauta mazauna ƙauyen.
Bayanai sun ce wanda lamarin ya shafa ya riga mu gidan gaskiya ne bayan an garzaya da shi wani asibiti da ke kusa domin ba shi kulawar gaggawa.
Wasu majiyoyi mazauna ƙauyen sun shaida wa Aminiya cewa, saurayin ya saba wasa da bindigar yana saita ’yan uwansa tamkar yadda yake gani ana ritsa mutane a wasan kwaikwayo, yana furta kalaman “da ka yi motsi zan harbe ka”.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe gomman sojojin Mali
Bayanai sun ce hatta a ranar da lamarin ya faru, suna zaune lafiya domin kuwa babu rashin jituwa tsakanin saurayin da kawun nasa, illa iyaka tsautsayi da ya ɗebi yaron mai wasa da bindigar ba tare da sanin an zuba alburusai a cikinta ba.
Wani makwabcin iyalan da abin ya shafa, ya bayyana cewa mahaifin mamacin mai suna Jamaica Konbofawei ne ya zuba alburusai a cikin bindigar yayin da ya ji motsin wasu dabbobi da suke shawagi a kusa da harabar gidansa.
Sai dai mutumin wanda ya yi rashin sa’a a farautar ta dare da ya fita, sai mantuwa ta sanya bayan dawowarsa da safiya ya ajiye makamin ba tare da zare ƙwanson alburusai da ya maƙala wa bindigar ba.
Makwabcin ya ce a haka yaron ya ɗauki bindigar kamar yadda ya saba ya kuma saita kawunsa a yayin da kawun ke roƙon da ya janye bakin bindigar amma kwatsam ya saki kunamarta kuma harsashin bindigar ya fita, lamarin da ya janyo masa ƙarar kwana.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Bayelsa, ASP Musa Muhammed wanda wakilinmu ya tuntuba, ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.