’Yan sa kai sun yi wa limami yankan rago a Zamfara

0
154

Jami’an tsaron sa kai na gwamnatin Jihar Zamfara (CPG) sun yi wa Babban Limamin Masallacin Juma’a na garin Mada, Imam Abubakar Hassan, yankan rago.

Wata majiya mai kusanci da marigayin ta ce jami’an sa kai biyar ne suka zo kauyen da ke Ƙaramar Hukumar Gusau a kan babura suka ɗauki marigayin bayan sallar La’asar ranar Lahadi.

“Lokacin da suka kama shi, mun yi tunanin ana gayyatar sa ne kan wata magana ko don gudanar da bincike, amma sai muka tsinci gawarsa a jefe a bayan gari.

“’Yan bangan sun yi wa limamin yankan rago ne. Ta yaya za a yi wa mutum irin wannan kisa?

“Marigayi shugaba ne mai natsuwa, kuma mai saukin kai, ba mu taba sanin sa da wani mummunan hali da zai sa a kashe shi ba.”

KU KUMA KARANTA: MƊD ta tabbatar da sace mata ’yan gudun hijira sama da 200 a Borno

Wani mazaunin garin, Muhammad Yunus ya bayyana kisan babban limamin a matsayin wani abu mai kama da siyasa ko bita da kulli.

Ya ce, Malam ya taba tsaya wa wadansu matasa biyu da ’yan banga suka kama bisa zargin su da hannu a fashi, bara.

“Na yi imanin wannan abin ne ya sa ’yan bangar, suka kashe Imam.

Babban kwamandan ’yan Sa Kai na Jihar Zamfara, Kanar Rabi’u Yandoto ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewara, kawo yanzu abin da aka iya ganowa shi ne ’yan sa kai na zargin sa da taimakawa masu garkuwa da mutane da satar shanu.

Kanar Yandoto ya bayyana cewa, hedikwatar CPG ba ta san komai game da kamun da aka yi wa babban limamin, inda ya kara da cewa “a ka’ida, idan muna zargin mutum muna kamo shi ne domin bincike, ba kashewa ba.

Don haka, wannan kisa ba bisa ka’ida aka yi ta ba, an aikata haramun kuma za a yi bincike.

“Ba mu ba jami’anmu umarnin kama kowa ba, don a yanzu haka jami’an CPG biyu da ake zargi da kisan babban limamin suna hannun mu; daga Mada aka kawo su kuma za mu yi musu tambayoyi bisa zargin da ake musu.”

Leave a Reply