Wata Kotu a Accra babban birnin ƙasar Ghana ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 17 ga wasu manyan jami’an ƙungiyar ‘yan a-ware ta Western Togoland Restoration Front (WTRF), ɗaurin shekara 17 a gidan yari.
Hukuncin nasu da aka yanke a ranar Laraba ya zo ne bayan da Mai Shari’a Mary Maame Ekueh Nyanzuh ta Babbar Kotun birnin Accra ta samu mutanen hudu da laifuka da dama.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da tsofaffin jami’an ƴan sanda da na soja.
Zarge-zargen da ake tuhumarsu da shi sun haɗa da: kasancewa mambobin haramtacciyar ƙungiya da kiran taron haramtacciyar ƙungiya da halartar taro, da bayar da gudunmawa don amfanin haramtacciyar ƙungiya.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya
An yanke wa wanda ya kafa ƙungiyar WTRF, Michael Koku Kwabla, wanda aka fi sani da Togbe Yesu Edudzi, daurin shekaru biyar a gidan yari, da kuma tarar cedi na Ghana 12,000 kwatankwacin dala 940.
Sauran mutane ukun da ake zargin Nene Kwaku da Emmanuel Afedo, da Abednego Mawena, an yanke musu hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari kowanne, da kuma tarar cedi 4,800, kwakwatancin dala 375 kowanne.
Lauyan da ke kare Andy Vortia ya roki a sassauta hukunce-hukuncen da ake yi wa wadanda yake karewa, yana mai cewa tuni suka shafe shekaru uku a tsare.
Masu gabatar da ƙara, ƙarƙashin jagorancin Joshua Sackey, sun yi adawa da ƙarar sassaucin hukuncin, inda suka bukaci kotun da ta zartar da hukunci mai tsauri don daƙile masu son aikata irin wannan laifin.
A ranar 25 ga Satumba, 2020, mambobin WTRF sun tare tituna a arewacin Ghana tare da ƙona wasu motocin jama’a guda biyu.
A ranar ne wasu ‘yan kungiyar suka kai hari a ofisoshin ‘yan sanda da ke yankin tare da kuɓutar da waɗanda ake tsare da su.
WTRF ƙungiya ce da ta ɓalle daga Gidauniyar Nazarin Gida, wacce babbar manufarta ita ce ɓallewa daga Jamhuriyar Ghana, da kafa kasa mai cin gashin kanta.
Kungiyar dai na neman iko da yankunan Oti da Volta a arewacin kasar, da kuma gabashin kasar Ghana.