Hukumar da ke sanya ido kan sufurin jiragen sama a ƙasar Kenya ta tabbatar da cewa jirgin Fasinja na Safarilink ya yi karo da wani jirgin da ke atisaye a sama.
An fara bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin.
“An fara bincike mai zurfi ta bangarorin hukumomi da dama, wanda ma’aikatar binciken hatsarin jiragen sama za ta jagoranta da kuma hukumar ƴansanda ta ƙasa don gano musabbabin hatsarin,” a cewar hukumar sa ido a kan sufurin jiragen sama na ƙasar.
KU KUMA KARANTA: Mutum 6 sun rasu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Ebonyi
Mutane biyu da ke cikin jirgin da ke atisayen duk sun mutu, amma an samu ceto fasinjoji 39 da ma’aikatan jirgin Safarilink biyar.
Kamfanin jiragen Safarilink ya bayyana a shafinsa na X cewa, jim kaɗan bayan tashin jirgin ne da misalin ƙarfe 3. 45 agogon ƙasar, aka yi wata ƙara mai ƙarfi.