Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 30,534 yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare

Aƙalla Falasɗinawa 30,534 aka kashe a yayin yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce aƙalla mutum 124 ne suka mutu yayin da wasu 210 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da wasu 71,980 suka samu raunuka tun bayan yakin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin Hamas.

KU KUMA KARANTA: Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta yi ƙira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, Isra’ila ta aikata kisan kiyashi 13 a Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *