Soke lasisin dubban kamfanonin canji ba zai kawo maslaha ba – ‘Yan Canji

0
89

‘Yan kasuwar canjin kuɗi da dama sun nuna rashin gamsuwa da soke lasisin sama da kamfanonin canji 4,000 da babban bankin Najeriya CBN ya yi.

Matakin dai ya ƙara jawo ƙorafi daga masu canjin da ke cikin barazanar fuskantar samamen jami’an tsaro da ke zargin su da tada farashin dala.

Duk da ɗaukar matakin yajin aiki na wuni ɗaya da kasuwar canjin ta yi don barranta kanta da hannu a tashin farashin, hakan bai hana ƙarin matakai masu tsauri kan ‘yan canjin ba.

Alhaji Sani Danmasanin Dogon Daji da ke cikin waɗanda aka soke mu su lasisi, ya ce ya cika ƙa’idojin da su ka dace amma bai tsira daga dirar mikiyar babban bankin ba.

Alhaji Sani ya ce wannan abin da CBN ya yi ya kamata ya tsaya ya yi nazari ya sake dubawa, saboda mutane da yawa sun bi ƙa’idojin da babban bankin ya bayar, amma sunayensu bai fito ba a jerin sunayen da suka fitar.

Shugaban ƙungiyar kasuwar canji ta Abuja, Alhaji Abdullahi Abubakar Dauran, ya ce su na biyaiya ga matakan gwamnati, amma ba su da hannu ko kaɗan a tashin farashin “mu ko nawa dala ta kama za mu yi kasuwancin mu don in ta sauko ma mun fi samun riba.”

KU KUMA KARANTA:Tashin farashin dala na daga cikin manyan matsalolin Najeriya – ƙwararru

Shi kuma shugaban ‘yan arewa mazauna kudu, Ambasada Musa Sa’idu, ya ce ba batun canjin kudi ne ya jefa Najeriya cikin tsada ba; hakan na da nasaba da jibgin bashin da gwamnatin Tinubu ta gada.

Gwamnan babban bankin CBN Olayemi Cardoso, ya dawo da tsarin ba wa ‘yan canji dala don daidaita farashin saɓanin yanda tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele ya dakatar da hulɗa da ‘yan canjin da zargin su da tallafawa almundahana da ƙungiyoyin ta’addanci.

Cardoso ya yi alwashin ɗaukar matakan rage tashin farashi da yanzu ya ke fiye da kashi 29 cikin 100 a Najeriya zuwa kashi 21.4 cikin 100.

Leave a Reply