No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun jagoranci ƙulla yarjeniyoyi daban-daban tsakanin ƙasashen biyu ranar Lahadi a birnin Doha.

Ƙasashen biyu sun sanya hannu kan jarjeniyoyin da suka shafi harkokin “ilimi da zuba jari da inganta rayuwar matasa da harkokin ma’adinai da harkokin yawon buɗe ido da wasanni,” in ji wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban Nijeriya ya fitar.

Gabanin bikin sanya hannu kan yarjeniyoyin a Fadar Shugaban Ƙasar Qatar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa mai masaukin baƙi cewa a shirye gwamnatinsa take ta yi maraba da masu zuba jari a ƙasar, yana mai yin nuni da sauye-sauyen da yake gudanarwa waɗanda za su taimaka wurin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da samun tagomashi a harkar zuba jari da kyautata al’adu.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Saudiyya ta haramata abubuwa 8 a azumin bana

“Babban jarinmu shi ne al’umarmu. Ƙarfinmu ya ta’allaƙa kan ƙwazon matasan Najeriya. Suna da kuzari da basira da jajircewa. Za su kasance abokan hulɗa a masana’antun Qatar.

Suna da ilimi da nagarta, kuma suna neman inganta kowane tsari da suka samu,” a cewar Shugaba Tinubu.

Shugaban na Najeriya ya jinjina wa gwamnatin Qatar bisa sauye-sauye da ci-gaban da take samu, yana mai cewa babban burinsa shi ne Najeriya ta samu irin wannan tagomashi.

“Mun gani ƙarara yadda Qatar ta samu ci-gaba cikin sauri. Ba zai yiwu mutum ya kawar da kai daga irin wannan nasara da kuka samu ba. Shugabannin wannan ƙasa sun yi abin da ya dace, kuma mu ma mun zo nan ne domin mu yi koyi da ku,” a cewar Shugaba Tinubu.

A nasa ɓangaren, Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya jaddada cewa a shirye ƙasarsa take ta yi maraba da batun zuba jari da Shugaba Tinubu ya gabatar, yana mai cewa ya je Najeriya a 2019 saboda muhimmancinta a harkokin ci-gaban duniya.

“Ba ni da shakku game da jajircewar al’ummar Najeriya. Duk duniya ta san irin ƙwazonsu da aiki tuƙuru. Abin da ya rage kawai shi ne mu ga sun aiwatar da hakan a cikin Najeriya ba a wajenta ba,” in ji shi.

Nan-take Shugaba Tinubu ya wakilta Ministan Harkokin Kuɗi, Mr. Wale Edun a matsayin jagoran tawagar gwamnati Nijeriya wadda za ta tattauna da ɓangaren Qatar kan tsarin zuba jari da yadda za a aiwatar da shi.

Kazalika shugaban Najeriya ya umarci Ministan Ma’adinai Dele Alake da ya gabatar da taƙaitaccen bayani game da ɗimbin ma’adinai da ake da su a ƙasar, ciki har da ma’adinin lithium.

Daga nan ne kuma ƙasashen suka sanya hannu kan yarjeniyoyi bakwai a fannin ilimi; tsarin gwamnatin Qatar na ɗaukar ma’aikata; haɗin-gwiwa don kafa majalisar kasuwanci (JBC) tsakanin cibiyar kasuwanci ta Qatar da takwararta ta Najeriya, Ma’adanai, da aikin gona; baya ga yarjejeniya kan matasa da wasanni.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...