Ƴan sandan Isra’ila sun kama masu zanga-zangar neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza

0
144

Ƴan sandan Isra’ila sun kama mutum bakwai daga cikin masu zanga-zanga saboda yin tarzoma a kusa da Titin Begin don neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

“Jam’ain ƴan sandan Isra’ila sun kama mutum 7 a Dandalin Kaplan da ke birnin Tel Aviv bisa zarginsu da yin tarzoma a yayin zanga-zangar da ke neman gwamnati ta sasanta da ƙungiar Hamas domin ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza,” in ji jaridar Yedioth Ahronoth.

Ta ƙara da cewa wasu masu zanga-zanga sun toshe hanyar da ake kira Begin Street — wata hanya mai matuƙar muhimmanci a Tel Aviv — a wani ɓangare na ƙoƙarin matsa lamba kan gwamnati don ta ɗauki mataki.​​​​​

A Yammacin Birnin Ƙudus, ɗaruruwan ƴan Isra’ila sun yi zanga-zanga a kusa da gidan Firaiminista Benjamin Netanyahu, inda suka buƙaci ya yi sulhu da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe mata da yara sama da 25,000 a Gaza — Pentagon

Kazalika masu zanga-zangar sun yi kira a gudanar da zaɓe ba tare da ɓata lokaci ba, a cewar Yedioth Ahronoth.

A yankin Caesarea da ke arewacin Isra’ila, mutum kimanin 1,200 sun yi zanga-zanga a kusa da gidan Netanyahu, inda suka buƙaci a saki mutanen da aka yi garkuwa da su sannan ya sauka daga mulki, kamar yadda kafar watsa labaran gwamnatin Isra’ila ta rawaito.

Masu zanga-zangar sun riƙa yin ihu suna sukar gwamnatin Netanyahu inda suka dinga maimaita cewa, “A gudanar da zaɓe nan-take!”

Haka kuma dubban Isra’ilawa sun yi zanga-zanga a wasu yankuna na ƙasar, ciki har da Haifa, Raanana da Rehovot.

Leave a Reply