No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan sanda sun kama wasu musu uku kan zargin ƙerawa kuma da sayar da makamai ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Binuwe.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Binuwe, Emmanuel Adesina, ya ce ana kama masu ƙera haramtattun makaman ne a yankin ƙaramar hukumar Vandekiya.

Ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar a ranar Laraba cewa, “bayan samun bayanan sirri ne jami’anmu na farin kaya suka kama mutum na farko.

“A yayin bincike an gano tare da ƙwace kananan bindigogi uku ƙirar gida a hannunsa.

KU KUMA KARANTA: Babban hafsan tsaron ƙasa ya zargi wasu ƙasashe da rashin adalci na ƙin sayar wa Najeriya makamai

“Shi ne ya jagoranci jami’an namu zuwa maboyar wasu maƙera biyu da ke sayar masa da bindigogin da suka ƙera, su ma aka kama su.

“Nan gaba za a gurfanar da dukkansu a gaban kotu,” inji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...