Amurka za ta fara jefa kayan agaji ta jirgin sama a Gaza bayan da yawan waɗanda suka mutu a yaƙin ya kai 30,000

0
97

Gwamnatin shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, na duba yiwuwar fara jefa kayan agaji ta daga sama a yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, a daidai lokacin da isar da sako ta ƙasa ke ƙara matuƙar wahala, kamar yadda wata kafar yada labarai ta Amurka Axios ta rawaito, inda ta ambato wasu jami’an Amurka hudu.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa Axios cewa “Halin da ake ciki ya yi muni ƙwarai da gaske. Ba za mu iya samun isassun agaji ta hanyar mota ba saboda haka muna buƙatar tsauraran matakai kamar saukar jiragen sama.”

KU KUMA KARANTA: Amurka ta ce Isra’ila ba ta gabatar da shirin kare fararen hula ba ta kutsa Rafah

Kazalika agajin jinƙai kaɗan ne ya shiga Gaza da aka yi wa ƙawanya a wannan watan, inda aka samu raguwar kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Janairu, in ji shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) a ranar Litinin.

Ya lissafo wasu daga cikin abubuwan da ke kawo cikas wajen kai kayan agaji da suka hada da rashin ƙoƙarin yin hakan daga shugabanni da rufe wuraren da ake bi a kai kayan, da kuma rashin tsaro, sakamakon mamayar sojoji da rushewar zaman lafiya.

Leave a Reply