Ƴan sanda a Kano sun kai mutanen da ake zargi da sayar da dala ba bisa ƙa’ida ba kotu

0
196

Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta gurfanar da wasu mutane da ta kama bisa zargin sayar da dalar Amurka ba bisa ƙa’ida ba a gaban kotu.

Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da daddare.

Ya ce rundunarsu tare da haɗin gwiwar hukumar EFCC, mai yaƙi a masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati da hukumar Kwastam sun kai samame a wasu wurare da ake hada-hadar dala ba bisa ƙa’ida ba a cikin birnin Kano a makon jiya inda suka kama mutum talatin da ɗaya.

A cewarsa an kai samamen ne a ” Wappa Bureau De Change, Ƙaramar hukumar Fagge da Bayan ofishin CBN da ke Ƙaramar hukumar Nassarawa da Central Hotel, Bompai Road, Ƙaramar hukumar Nassarawa da Ashton Road da Filin Jirgin saman Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano (MAKIA) da Ƙofar Ruwa Motor Park, Ƙaramar hukumar Dala da Kasuwar Hatsi ta Dawanau a Ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.”

KU KUMA KARANTA: EFCC ta tsare masu sayar da sabbin takardun kuɗi a Kano

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce cikin mutanen da aka kama an sallami mutum 22 saboda babu wata shaida da ta nuna sun aikata laifi, yana mai cewa an kama mutum tara da kuɗaɗen ƙasashe daban-daban da suka haɗa da dalar Amurka da naira da kuɗin ƙasar Masar da kuɗin ƙasar Habasha da sauransu.

“An gurfanar da mutum tara da ake zargi gaban kotu mai lamba 70 da ke Normandsland a Kano domin su fuskanci hukunci,” in ji Kiyawa.

A makon jiya ne gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaron ƙasar za su haɗa gwiwa domin soma yin dirar mikiya kan mutanen da ke sanya dala ta yi tsada a ƙoƙarinta na magance matsalolin da ke kawo tarnaƙi ga tattalin arzikin ƙasar.

Leave a Reply