Hukumar hana fasa-ƙwauri a Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu mutane sakamakon turmutsutsu lokacin da suke ƙokarin sayen shinkafa mai rahusa da take sayarwa a birnin Lagos da ke kudancin ƙasar.
Hukumar ta bayyana haka ne ranar Litinin da maraice a wata sanarwa da mai magana da yawunta Abdullahi Maiwada ya fitar.
Sanarwar ba ta faɗi adadin mutanen da suka mutu ba, kuma Maiwada ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa ba alhakin hukumarsu ba ne bayyana yawan mutanen da suka rasu ko suka jikkata.
Sai dai sanarwar da ya fitar ta ce an samu turmumutsin ne bayan shinkafar da ake sayarwa ta ƙare abin da ya sa suka sanar da mutane cewa za a ci gaba da sayarwa washegari.
“Mutanen da suka taru sun ɗimauce sannan suka ture shingayen da aka sanya inda suka je kwantainonin da babu komai a cikinsu domin neman shinkafa. Hakan ne ya haddasa turmutsutsi, abin da ya kai ga rasa rayuka da kuma jikkatar wasu,” in ji Maiwada.
KU KUMA KARANTA: Tsadar rayuwa: Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘yankasuwan Najeriya
Hukumar ta Kwastam ta yi ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu sannan ta sha alwashin gudanar da bincike kan lamarin.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumar ta soma sayar da shinkafa a farashi mai rahusa, inda take sayar da buhu mai kilogiram 25 a kan naira dubu goma wanda a kasuwa ake sayarwa a kan naira 40,000.