Tsadar rayuwa: Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘yankasuwan Najeriya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da manyan ‘yankasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki da kuma tsadar rayuwar da ‘yanƙasar ke fuskanta.

Taron ya kuma tattauna kan yadda darajar kuɗin ƙasar, Naira ke faɗuwa yayin da darajar dalar Amurka ke ƙara tashi, a yayin ganawar ta ranar Lahadi.

Baya ga batun tattalin arziƙi taron ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi wadata ƙasar da abinci da kuma na tsaro.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa “kamar yadda na sha faɗa al’ummar ƙasar nan su ne kaɗai mu ke da su, kuma muke son kyautatawa, mun damu matuƙa da halin da suke ciki”

Cikin waɗanda suka halarci taron a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, sun haɗa da attajirin ɗankasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga saboda tsadar rayuwa ba mafita ba ce — Sarkin Musulmi

“Mun tattauna kan batun samar da ayyukan yi da wasu batutuwa da dama… abin alfaharin shi ne Najeriya ƙasa ce mai albarka, kuma mu na da kyakkayawan fata kan za mu iya sauya tattalin arziƙinmu kuma za mu tabbatar da hakan.” In ji Ɗangote.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ke shirye-shiryen yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Miliyoyin ‘yan ƙasar ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci da yunwa, lamarin da ake alaƙantawa da cire tallafin mai da kuma sauran gyaran fuskar da shugaban ƙasar ya yi tun bayan hawansa mulki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *