Mutum 15  sun mutu a harin da ƴan bindiga suka kai coci a Burkina Faso

0
173

Fararen-hula aƙalla 15 ne suka mutu sannan biyu suka jikkata a wani harin “ta’addanci” da aka kai a cocin Katolika da ke arewacin Burkina Faso ranar Lahadi, a cewar wani babban jami’in cocin.

“Muna sanar da ku cewa an kawo harin ta’addanci a cocin Katolika da ke ƙauyen Essakane yau, 25 ga watan Fabrairu, yayin da mutane suka haɗu suna gudanar da ibada,” in ji shugaban cocin Dori, Jean-Pierre Sawadogo, a wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ƙara da cewa mutanen da suka mutu sun kai 15 sannan mutum biyu sun jikkata.

Sawadogo ya yi ƙira da a zauna lafiya a Burkina Faso sannan ya soki waɗanda ya ƙira “mutanen da ke ci gaba da kashe jama’a da raba kan ƙasarmu”.

KU KUMA KARANTA: Mali da Burkina Faso sun miƙa wa ECOWAS wasikar ficewarsu

Ƙauyen Essakane yana kan iyakar ƙasar da Mali da Jamhuriyar Nijar.

Wannan shi ne hari na baya bayan nan da ake ɗora alhakin kai shi kan ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi a yankin, waɗanda kan kai hare-hare a coci-coci sannan a wasu lokutan suna sace malaman cocin.

Burkina Faso na da faɗin ƙasa a yankin Sahel, inda masu iƙiradin jihadi suka matsa ƙaimi wajen kai hare-hare tun bayan faɗuwar gwamnatin Libya a 2011 da kuma ƙwace iko da masu iƙirarin jihadi suka yi da arewacin Mali a 2012.

Waɗannan hare-hare sun watsu zuwa maƙwabciyarsu Jamhuriyar Nijar.

Shugaban mulkin sojin ƙasar Kyaftin Ibrahim Traore, wanda ya ƙwace mulki a 2022, ya sha alwashin murƙushe masu tayar da ƙayar baya, amma har yanzu lamarin ya gagara.

Alƙaluma sun nuna cewa an kashe mutum fiye da 20,000 a hare-haren da masu tayar da ƙayar baya suke kai wa Burkina Faso sannan an raba sama da mutum miliyan biyu da muhallansu.

Leave a Reply