Najeriya ta maida wa Nijar wutar lantarki

0
100

Najeriya ta amince ta maido da wutar lantarki da ta yanke wa Jamhuriyar Nijar bayan ƙungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakaɓawa ƙasashen Nijar din da Mali da Burkina Faso kuma Guinea.

ECOWAS ta dage takunkumin ne bayan babban taron kungiyar kan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro da ya gudana a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Tinubu, ya ce, saboda haka “Najeriya sa ta dawo da wutar lantarki da ta yanke wa Nijar ba tare da bata lokaci ba.”

A watan Agustan bara ne Najeriya ta katse wutar lantarki da take ba wa Nijar a matsayin wani bangare na takunkumin da ECOWAS ta kakaɓa saboda juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.

Al’ummar Nijar, musamman mazauna manyan birane sun shiga damuwa saboda rashin wutar lantarkin.

A watan Nuwamba ne dai sanatoci daga Arewacin Najeriya suka bukaci Tinubu ya mayar wa Nijar wutar.

A ranar Asabar kuma shugaban da kansa ya yi kira da ECOWAS ta dage jingine tattalin arzikin da ta kakaɓawa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea.

KU KUMA KARANTA: Al’ummar Nijar na maraba da matakin ECOWAS na janye musu takunkumi

A cewarsa, an sanya takunkumin ne da nufin shawo kan shugabannin gwamnatocin sojin ƙasashen zuwa teburin tattaunawa.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta ɗauki matakinta ne bisa kyawawan manufofin yankin na tsaro, zaman lafiyar al’umma, mulkin dimokuraɗiyya, ’yancin siyasa, yalwar arziki da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar samar da dama ga kowa a yammacin Afirka.

Ya ce babu wata ƙiyayya ko boyayyar manufa a cikin matakan da aka dauka kuma babu wata manufa ta ruguza halastacciyar manufar siyasa ta kowace kasa ko cigaban wani ɓangare.

Da haka ne Tinubu ya buƙaci ƙungiyar da ta saukaka shigar da kayayyakin abinci da magunguna da sauran kayayyakin jin kai ba tare da katsewa ba ga al’ummar waɗannan ƙasashe, musamman ma waɗanda suka fi kowa rauni.

Leave a Reply