Ƴan bindiga sun kashe sojojin Nijar huɗu a kusa da iyakar Najeriya

0
137

Sojojin Nijar huɗu sun mutu a wani samame da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai kusa da kan iyakar Nijeriya, kamar yadda gidan talabijin ɗin ƙasar ya sanar a jiya Juma’a.

“Ƴan bindiga a kan babura kusan 100 ne suka kai hari kan jami’an jandarma,” a wani sansanin soji da ke Bassira, wani ƙauye da ke kan iyaka a yankin Maradi, kamar yadda wani jami’in siyasa na yankin ya shaida wa AFP.

Harin dai ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu sannan biyu kuma sun jikkata, daga cikin jami’an rundunar tsaro ta Nijar FDS, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta faɗa, yayin da wata mata ta samu rauni sakamakon kuskurar ta da harsashi ya yi.

Bayan shafe awa guda ana musayar wuta, dakarun FDS sun fatattaki maharan, waɗanda suka kwashe ƴan’uwansu da suka mutu da waɗanda suka jikkata, amma sun bar baburansu guda uku da na’urorin sadarwarsu da kuma makamai, a cewar rahoton.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Nijar ta karya farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50

“Hari ne da ba a cika samun irinsa ba a yankin,” a cewar ɗan siyasar, inda ƴan bindiga suke yawan kashe mutane da sace-sace da tayar da hankalin al’ummar yankin.

“A yanzu waɗannan mutanen ba masu satar shanu ba ne kawai da muke fama da su…, kamar yadda gwamnan yankin Maradi, Issoufou Mamane, ya shaida wa gidan talabijin ɗin bayan ziyarar da ya kai wajen da aka yi harin.

“Ba za mu bari wannan harin na matsorata da dabbanci ya tafi ba tare da ɗaukar mataki ba.”

Yankin dai yana ɗaukar baƙuncin ƴan gudun hijira daga Najeriya fiye da 46,000, waɗanda suka tsere daga rikicin ƴan bindiga da suka addabi kan iyakar a tsawon shekaru, kamar yadda alƙaluman hukuma suka nuna.

Ƴan fashin, waɗanda ke ɓuya a cikin dazuzzuka, sukan kai farmaki a kan iyakar da ke da nisan kilomita 1,600 a tsakanin ƙasashen biyu.

Dakarun ƙasashe suna jagorantar ayyukan haɗin gwiwa don ƙoƙarin daƙile hare-haren, a hannu guda kuma dole ne su tunkari mayaƙan Boko Haram da kuma ƙungiyar IS ta Yammacin Afirka.

Leave a Reply