Za’a buɗe sabuwar ma’aikatar wutar lantarki a jihar Abiya

0
128

Kamfanin Geometric Power Ltd na gab da buɗe sabuwar tashar wutar lantarki mai zaman kanta a garin Osisioma da ke yankin Aba na jihar Abia, wacce za ta samar da megawatt 188 na wuta daga iskar gas, yayinda ake ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin wutar lantarki a sassa daban daban na Najeriya,.

Tsohon Ministan lantarki da kuma Shugaban kamfanin Ferfesa Barth Nnaji ne ya shaida wa Muryar Amurka hakan, tare da cewa aikin zai lashe kimanin dala miliyan ɗaya.

Farfesa Nnaji ya ƙara da cewa, “Aikin zai yi tasirin gaske, saboda an tsara aikin ne don samar da ingantacciyar wutar lantarki ga birnin Aba da ƙananan hukumomi 9 na jihar Abia, masu faɗin fili kimanin murabba’in kilomita 4000, da yawan jama’a sama da miliyan ukku. Aikin zai farfaɗo da masana’antu da dama, da kuma tada komaɗar tattalin arziƙin yankin kudu maso gabas.”

A nashi bayanin, kakakin kamfanin C Don Adinuba, “Muna amfani ne da injin turbin huɗu daga General Electric, wanda shi ne kamfani mafi girma a duniya a sarrafa kayayyakin lantarki. Abin da yankin Aba ke buƙata shi ne kimanin megawatt 100 don inganta harkokin kasuwanci, da yake akwai manyan masana’antu a Aba da ke kashe maƙudan kuɗi wajen samun wutar lantarki. Yanzu da shigowar mu, za su riƙa samun wutar lantarki daidai gwargwado don raya harkokin su.”

KU KUMA KARANTA:Kotu ta umurci CBN ta biya wani Bajamushe naira Miliyan 63 da ta tsare ba bisa ƙa’ida ba

Adinuba ya ƙara da cewa tashar za ta taimaka sosai wajen rage tsadar sarrafa kayayyaki a yankin Aba, tare da rage tsadar kayayyaki ta yadda al’ummar Najeriya baki ɗaya za su amfana.

Tuni gwamnatin jihar Abia ta yi marhabin da aikin, tare da kamanta shi a matsayin wanda zai kawo muhimmin sauyi a lamuran jihar.

“Wannan ya yi ma’ana sosai, saboda al’ummar mu sun daɗe suna fama da ƙarancin wuta, musamman a yankin Aba. Kuma da zarar tashar ta fara aiki, masana’antu da yawa za su farfaɗo,” inji kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Okey Kanu.

Yanzu masana na ci gaba da kamanta wannan aikin Geometric Power Plant a matsayin jari mafi girma a duk kudu maso gabashin Najeriya, kuma ana sa ran cewa shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da tashar a ranar Litinin mai zuwa.

Leave a Reply