No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta karya farashin kuɗin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, wanda a da kudinsa yake jaka 16.500 ta CFA, a yanzu kuma za a ringa sayar da shi jaka 13.500.

Ma’aikatar Kasuwanci ta Ƙasar ce ta sanar da hakan a yayin wani taro da Ministan, Malam Asmane Saidou ya gudanar tare da ƙungiyoyin ƴan kasuwar ƙasar.

Sai dai wannan sabon farashi ya bambanta daga wannan jihar zuwa wata, inda a Yamai za a sayar da buhun a kan jaka 13.500 na CFA.

Farashin sauran jihohin sun haɗa da:

Dosso 13.675 CFA

Tawa 13.825 CFA

Maradi 13.925 CFA

Zinder 14.000 CFA

Diffa 14.375 CFA

Agadez 14.125 CFA

Atillaberi 13.650 CFA.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan ta zauna da ƴan kasuwar masu manyan motocin dakon kaya aka tattauna da su kafin ɗaukar wannan matakin.

KU KUMA KARANTA: DSS ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya a kan shirin zanga-zangar ‘tsadar rayuwa

Sai dai gwamnatin ta ja hankalin ƴan kasuwar da su mutunta wannan farashin da aka tsayar.

Nijar tana shigar da shinkafa daga ƙasashen waje ne inda ƴan kasuwa ke amfani da tashar ruwan Tekun Jamhuriyar Benin wajen shigar da kayayyakinsu zuwa cikin ƙasar.

To sai dai juyin mulkin da sojojin kasar sukayi a watan yulin bara ya sa Jamhuriyar Benin rufe iyakokinta da Nijar bisa umurnin Ƙungiyar Ecowas, wadda ta ƙaƙaba wa Nijar takukumai, lamarin da a baya ya haddasa ƙarancin shinkafar da sauran ƙayan masarufi, da kuma tashin farashinta a kasuwanni.

Amma rahotanni daga Nijar ɗin na cewa a yanzu abubuwa sun fara daidaita ba kamar watanni shida na baya ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...