Gwamnatin Legas za ta fara ciyar da mutane dafaffen abinci kyauta

0
91

Gwamnatin Jihar Legas ta sanar da cewa za ta fara raba wa mutane dafaffen abinci kyauta sau ɗaya a kowace rana.

Mai bai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara kan watsa labarai Jubril A Gawat ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Ya ce gwamnatin za ta yi wannan aiki ne ta hanyar neman masu abincin sayarwa da za su dinga dafa abincin mutum 1,000 a kowace ƙaramar hukuma.

Wannan mataki na gwamnatin na zuwa ne a lokacin da al’ummar Najeriya ke kokawa kan matsalar ƙarancin abinci saboda tsadarsa sakamakon hauhawar farashi.

Masu sharhi na danganta hauhawar farashin da tashin da dala ke yi, inda darakar naira kuma ke yin ƙasa a kusan kowace rana.

KU KUMA KARANTA: Yaran Gaza sun yi zanga-zangar adawa da mamayar Isra’ila ta hana su abinci da ruwa

Baya ga matakin ciyar da jama’a dafaffen abinci da gwamnatin Jihar Legas ta sanar, ta kuma ce daga yanzu ta mayar da haihuwa a asibitocin gwamnatin kyauta.

“Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da yin haihuwa kyauta, ciki har da tiyata a asibitocin gwamnati da ma ba da wasu magungunan duka kyauta,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Leave a Reply