Ƙungiyar NARTO ta dakatar da yajin aikin gamagari, ta umarci ma’aikatan ta su koma bakin aiki

Ƙungiyar ta janye yajin aikin da ta fara ranar Litinin bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi tsakaninta da sauran masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur kamar NNPCL, NMDPRA, DAPPMA da dai sauran su.

Bayan shiga tsakanin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi ta ɓangaren Hukumar Kula da Dokokin man fetur, da ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ƙungiyar masu motocin dakon man fetur ta ƙasar wato NARTO, ta dakatar da yajin aikin gamagari da ta shirya daga jiya litinin 19 ga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki.

Wannan matakin dai ya biyo bayan ganawar da ƙungiyar da wasu masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur suka fara daga jiya Litinin ya zuwa maraicen yau Talata.

Mambobin ƙungiyar NARTO dai sun dakatar da ayyukansu na jigilar man fetur a faɗin ƙasar sakamakon tsadar man dizal da kuma matsin tattalin arziƙi a ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Babban hafsan tsaron ƙasa ya zargi wasu ƙasashe da rashin adalci na ƙin sayar wa Najeriya makamai

Mambobin ƙungiyar NARTO sun yi barazanar tsayar da ayyukan su cik a faɗin ƙasar tun daga jiya Litinin saboda tsadar man dizal wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da motocinsu a faɗin Najeriya.

Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi daga kan Naira ɗari 6 zuwa 7 kan kowace lita, farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a musamman a baya-bayan nan, lamarin da ba ya rasa nasaba da tashin farashin dala a kasuwannin bayan fage da na hukuma a ƙasar.

A yanzu dai ana sayar da man dizal sama da Naira dubu 1 da 250 akan kowace lita a Najeriya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *