NLC ta ce za ta shiga yajin aikin a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.
Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ayyana shirin gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Comrade Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar.
A cewarsa, ƙungiyar za ta yi zangar-zangar a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.
Ƙungiyar har ila yau ta ce za ta yi gangamin ne saboda taɓarɓarewar tsaro a sassan ƙasar.
Matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ta yi ƙamari a sassan ƙasar ciki har da birnin Abuja da fadar shugaban ƙasa ta ke.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya na neman wasu ma’aikatan CBN ruwa a jallo kan zargin satar dala miliyan shida
Ajaero ya ce zanga-zangar za ta wakana ne mako guda bayan cikar wa’adin makonni biyu da ƙungiyar ta bai wa hukumomin Najeriya wanda zai kare a ranar 23 ga watan Fabrairu.
Matsalar hauhawar farashin kayayyaki musamman na kayan masarufi ya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali yayin da darajar Naira ke ci gaba da faɗuwa.
Hukumomi sun ce suna ɗaukan matakan da suka dace ciki har da fito da abinci daga rumbunan gwamnati don a rabawa jama’a.
A makon da ya gabata, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni a fitar da tan 102,000 na shinkafa da masara daga rumbun adana abinci na tarayya.
A ranar Alhamis ya gana da gwamnonin jihohin ƙasar 36 don lalubo hanyoyi da za a magance matsalolin ƙasar.