Farashin kayayyakin masarufi na ci gaba da tashi a Najeriya

0
73

Farashin kaya a Najeriya na ci gaba da tashi babu ƙaƙƙautawa a farkon shekara nan, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta bayyana a rahoton da ta fitar.

Hukumar ta ce farashin kayayyaki ya yi matuƙar tashi a watan Junairun shekarar nan, inda farashin ya ƙaru da kaso 8.8 cikin ɗari, idan aka kwatanta da yadda farashin yake a watan Janairun shekarar 2023.

Rahoton ya ce farashin kayayyaki sun ci gaba da hauhauwa a farkon shekarar da aka shiga, fiye da yadda farashin yake a watan Disambar shekarar da ta gabata.

Hukumar NBS ta ce, farashin kayayyakin abinci a Najeriya ya yi matuƙar tashi a watan Janairun da ta gabata, inda farashin ya ƙaru kuma ya kai kaso 35.41 cikin ɗari bisa ma’auni, wanda hakan ya nuna cewa farashin ya ƙaru da kaso 11.10 cikin ɗari, idan aka kwatanta da yadda yake a watan Janairun shekarar 2023, inda farashin yake a matsayin kaso 24.32 cikin ɗari.

Farashin kayayyakin masarufi da sauran nau’ukan kayayyaki sun ci gaba da hauhauwa a ƙasar biyo bayan cire tallafin man-fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin kama rantsuwar aiki.

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya zamo wani abu da ‘yan ƙasar ke ta kokawa akai, wanda kuma hakan ya sa wasu ke rayuwa da abin kalace sau ɗaya a yini.

KU KUMA KARANTA:Masu Biredi a Najeriya na shirin tsunduma yajin aiki saboda tsadar kayan hada Biredi

A hirarsa da Muryar Amurka, Nasiru Shu’aibu Marmara masani kuma manazarci kan lamuran da suka shafi tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa, ya ce “yadda farashin kayayyaki yake tashi a Najeriya, babban barazana ne ga tattalin arziƙin ƙasar, duk da cewa anyi hasashen faruwar hakan, idan aka duba yadda aka ɗaura tubalin tafiyar da tattalin arziƙin ƙasar.”

Nasiru Shu’aibu ya ƙara da cewa “Gwamnati yanzu tana ƙoƙarin ganin ta ƙara samar da hanyar kuɗin shiga ga ‘yan ƙasar, domin ya zo daidai da yadda farashin kaya yake a ƙasar.”

Yanzu dai hankulan yan ƙasar ya karkata ne ga mahukunta, domin ganin yadda za su shawo kan lamarin.

Leave a Reply