Hisbah ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta akan maɗigo

0
176

Hukumar Hisba ta kama matashiyar budurwar nan mai suna Ramlat Princess, bayan ta tallata kanta a wani faifen bidiyo tare da yaɗa shi a shafukan sada zumunta a kano

Ramlat a cikin wani bidiyon ta na cin alwashin duk namijin da zai aure ta, sai ya auro mata wata macen da za ta dinga yin lalata da ita, ma’ana Lesbian.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta cafke Murja Ibrahim Kunya a Kano

Zuwa yanzu hukumar hisba ba ta bayyana matakin da za ta ɗauka kan Ramlat Princess ba.

Idan zaku tuna muƙaddashiyar babban kwamandan hukumar ɓangaren mata DR. Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana cewa za su ci gaba kama masu hawa shafin Tiktok suna furta kalaman batsa.

Leave a Reply