Ƙasashen Larabawa sun nemi MƊD ta dakatar da Isra’ila daga mamaye Rafah

0
147

Ƙasashen Larabawa 22 a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi ƙira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar ya nemi a tsagaita wuta nan-take a Gaza da kuma bari a kai kayan agaji da ma hana fitar da kowane Bafalasɗine daga yankin.

Jakadan Tunisia a Majalisar Tarek Ladeb ya bayyana “bala’in da ke fuskantar” Falasɗinawa miliyan 1.5 da ke yankin Rafah na Gaza muddin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aiwatar da shirinsa na mamaye yankin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah

Mako biyu da suka wuce Algeria ta raba wani daftarin doka wanda yake adawa da tursasa wa mutane barin yankinsu tare da neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza.

Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta bayyana damuwarta game da yiwuwar rugujewar tattaunawar tsagaita wuta.

Leave a Reply