An hana gudanar da zanga-zanga a Senegal

Hukumomi a Senegal sun hana ƴan hamayya yin zanga-zanga ranar Talata a yayin da Amurka ta bi sahun masu ƙira ga Shugaba Macky Sall ya gudanar da zaɓe sannan ya sauƙa daga mulki.

Mutum uku ne suka mutu tun lokacin da aka soma zanga-zanga a ƙasar bayan Shugaba Sall ya ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa watan Disamba.

A yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da matsa lamba kan Shugaba Sall don ya gudanar da zaɓe, wata gamayyar ƙungiyoyin fararen-hula da addinai da masana mai suna Aar Sunu Election (Dole mu kare zaɓenmu) ta yi ƙira a gudanar da zanga-zanga a Dakar.

Sai dai ta janye zanga-zangar har sai ranar Asabar, tana mai cewa hukumomin birnin Dakar sun hana ta yin gangamin suna masu cewa matakin zai kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.

An ga tarin jami’an ƴan sanda da aka jibge a wuraren da aka tsara gudanar da zanga-zangar.

KU KUMA KARANTA: Shugaban Senegal, Sall, ya kare matakinsa na ɗaga zaɓen ƙasar

Hukumomi sun katse intanet a karo na biyu tun da Shugaba Sall ya sanar da ɗage yin zaɓen. Ma’aikatar sadarwa ta ce ta ɗauki matakin ne saboda “masu yaɗa rahotannin ƙiyayya waɗanda tuni suka janyo zanga-zanga”.

Amurka da Faransa sun jaddada ƙira ga Shugaba Sall ya gudanar da zaɓe kamar yadda ya yi alƙawari.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ” ya yi magana da shugaban ƙasar Senegal da safiyar nan inda ya jaddada fargabarmu game da halin da ake ciki a can sannan ya bayyana masa ƙarara cewa muna so a gudanar da zaɓe kamar yadda aka tsara – muna so a gudanar da shi nan ba da jimawa ba,” a cewar kakakin Ma’aikatar Wajen Amurka Matthew Miller a hira da manema labarai a Washington.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *