No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga a sansaninsu da ke unguwar Mpape, a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce an kai samamen ne a ranar 9 ga watan Fabrairu bayan samun bayanan sirri.

Ya ce, sun yi nasarar kashe wasu kasurguman mahara a maɓoyar.

Ya ce sun hallaka kasurgumin ɗan bindigar da ya addabi yankunan Mpape, Bwari a Abuja, Kagarko a Kaduna, Masaka da kuma kauyen Nukun a Jihar Nasarawa.

A cewarsa, maharan sun jima suna satar mutane tare da karɓar kuɗin fansa.

KU KUMA KARANTA: Ina cikin waɗanda ƴan bindiga ke son kai wa hari — Dikko Radda

Kazalika, ya ce sun samu nasarar kai farmakin ne a maboyarsu da ke wani tsauni a Mpape tare da kwato makamai.

Adejobi, ya ce sun ƙwato makamai da suka haɗa da wayoyin hannu, layin waya, laya da kuma ƙwayoyi.

Ragowar sun haɗa da alburusai, adda, wuƙaƙe da sauran muggan makamai.

Adejobi, ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ya ce, rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don kama masu laifi, tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...