Tsadar abinci: Gwamnati za ta fara raba kayan abinci a faɗin Najeriya – Kwamiti

Gwamnatin Najeriya za ta fara ɗaukar matakin rage matsalar rashin abinci da tsadarsa a faɗin ƙasar biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da zanga-zangar da aka yi a wasu sassan ƙasar kan tsadar rayuwa.

Za’a raba ton 42 na kayayyakin abinci iri-iri waɗanda za a fitar daga runbunan ajiye abincin baya ga shinkafa tirela 2000 da za a sayo daga wurin ‘yan kasuwa don rabawa ma jama’a. Wannan bayanin ya fito ne daga wurin kwamitin Ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa biyo bayan ƙorafe-ƙorafe rashin abinci da kuma tsadarsa a faɗin Najeriya.

Kwamitin ya yanke wannan shawarar ce bayan zaman da ya yi na kwanaki uku don tattaunawa kan hanyoyin da za a ɓullo ma matsalar ƙarancin abinci da kuma tsadarsa a Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Najeriya ta ƙara shiga yanayin ƙarin haraji bayan cire tallafin Fetur

Mamban kwamitin kuma Ministan Yaɗa Labaran Najeriya, Alhaji Muhammad Idris, wanda bayan zaman kwamitin na uku ya yi ƙarin bayani a manema labarai.

To amma Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya, Alhaji Kabiru Ibrahim Faskari, ya ce ya kamata a haɗa irin wannan matakin da tsarin tallafa ma manoma da na’urorin zamani a farashi mai rahusa kuma ya zama tsari ne na dindindin ba sau ɗaya kawai ba ko kuma idan ta ɗauro kawai ba. Ya ce kodayake gwamnati ba ta da isasshen kuɗin da za ta tallafa ma mutane da kayan abinci kyauta, ya kamata shi ma kayan abincin a sayar ma talakawa a farashi mai rahusa.

Minista Idris ya gargaɗi ‘yan kasuwa da ke sayen kayan abinci su kuma ɓoye don su sayar daga baya da matuƙar tsada da su daina. Ya ce gwamnati ta san irin waɗannan ‘yan kasuwa kuma idan ta kama za ta ɗau mataki a kan su.

Ya ce tun da bayar wa kyauta na iya janyo rubibi da ruɗani a wuraren raba abincin, sayarwa a farashi mai rahusa zai ɗan rage rubibi da hargowa. Ya kuma ce ya kamata gwamnati ta tabbatar waɗanda ke matuƙar buƙata aka fi bai wa fifiko wajen rabawa, ba magoya bayan jam’iyya ba. Kuma a tabbatar duk wanda aka ba shi abincin bai sayar ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *