Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya yi alƙawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan’adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.
Ɗangote ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Jihar Kano, a ranar Juma’a, inda ya ce ya yi amanna talaka na cikin ƙunci kan halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.
Attajirin ya ce ya so yin wannan ziyara tun da jimawa amma yawan tafiye-tafiyensa suka sa sai yanzu ya zo.
Ɗangote ya yi alƙawarin tallafa wa Kano don inganta kiwon lafiya da ilimi da ƙarfafa wa masu ƙaramin ƙarfi da ke gwagwarmayar rayuwa, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan ganawar ta ce.
“Da farko dai mun zo nan ne don mu taya ku murnar nasarar da kuka samu a Kotun Ƙoli, ina so in tabbatar muku da goyon bayanmu a tsawon mulkinku, watakila ba shekara huɗu kawai ba har amma shekaru takwas.
KU KUMA KARANTA: Ban ce na fi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa ba — Ɗangote
Ɗangote wanda ya ce Kano gida ne a wajensa, duk da cewa mai gabatarwa a wajen taron ya bayyana shi a matsayin baƙar fatan da ya fi kuɗi a duniya, ya ce “Ni naku ne don haka koyaushe za ku iya kira na don hadin kai kan yadda za mu ciyar da Kano gaba.”
“Kuma a ci gaba da gaske muna buƙatar ganin yadda za mu bunƙasa fannonin kiwon lafiya da ilimi da ƙarfafa wa gwamnati, da ta yadda za mu taimaka wa gwamnati domin gwamnati ba za ta iya yin komai ita kaɗai ba”.
Ɗangote ya ci gaba da shaida wa Gwamna Abba cewa “Akwai haƙƙin mutane a kanku kuma a yanzu jama’a na cikin matsi. Don haka a yanzu ku ne za ku zama majinginar mutane mu kuma za mu taya ku ji da su.
“Don haka ku tabbata cewa za mu ba ku goyon baya kuma za mu goyi bayan gwamnatinku, kuma muna so mu gaya muku cewa za mu ci gaba da yi muku addu’ar samun nasara domin nasararku tamu ce.
A nasa ɓangaren, Gwamna Yusuf Yusuf ya nemi goyon bayan attajirin kan kafa cibiyar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfaɗo da masana’antun da suka lalace da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Hakazalika, Gwamnan ya shaida wa Ɗangote Kano cewa yana matukar bukatar a kafa asibitin masu cutar sikila a jihar domin samar da magunguna kyauta ga marasa lafiya.
Baya ga haka, sanarwar ta ce Abba Gida-Gida ya roƙi hamshaƙin ɗan kasuwan cewa “ka daure ka kammala manyan ayyukan da gidauniyarka ta Dangote ta ƙaddamar wadanda suka hada da sashen gaggawa da ɗakin tiyata da sashen mata masu juna biyu da na yara duk a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhamnad.”