‘Yan wasan Najeriya sun yi jimamin waɗanda suka mutu a kallon wasan su da Afirka ta Kudu

0
122

Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasa na Najeriya yayin zaman nuna jimamin waɗanda suka mutu a lokacin kallon wasan ƙwallon ƙafa da tawagar ta yi da Afirka ta Kudu, inda aka yi tsit na ɗan wani lokaci don yi wa mamatan addu’a.

‘Yan wasan Najeriya na Super Eagles sun nuna jimaminsu ga waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin da Najeriya take karawa da ‘yan wasan Afirka ta Kudu a wasan dab da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.

Rahotanni da dama daga Najeriya sun ruwaito mutuwar aƙalla mutum biyar yayin da aka yi fafatawar mai zafi wacce ta da hankulan masu kallo musamman lokacin da aka shiga zangon bugun fenariti.

Wasan wanda aka buga a ranar Laraba a birnin Bourke na ƙasar Ivory Coast ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi da ci 1-1 duk da ƙarin lokaci da aka yi.

A ƙarshe Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da ci 4-2 a bugun na fenariti. Wannan nasara ta ba ‘yan wasan na Super Eagles damar zuwa wasan ƙarshe a gasar.

KU KUMA KARANTA:Yadda Ahmed Musa, captain ɗin Super Eagles, ya rabawa mata da matasa tallafi

Najeriya za ta haɗu da Ivory Coast mai masauƙin baƙi a wasan ƙarshe a ranar Lahadi.

Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasa na Najeriya yayin nuna zaman nuna jimamin inda aka yi tsit na ɗan wani lokaci don yi wa mamatan addu’a.

“In Allah ya yarda, za mu daga wannan kofi a ranar Lahadi wanda za mu sadaukar ga wadanda suka mutu.” In ji Musa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ga wasu daga cikin ‘yan Najeriya waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin wasan kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito:

Mai kula da sha’anin kudi na Jami’ar Jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi
Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jami’yyar APC mai mulki, Dr. Cairo Ojougboh
Dan kasuwa/Dan Najeriya mazaunin Ivory Coast, Chief Osondu Nwoye
Mazaunin jihar Ogun, Mikail Osundiji
Mai aikin bautar kasa a jihar Adamawa, Samuel (babu cikakken bayani kan sunan mahaifinsa)

Leave a Reply