Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta shirya da Isra’ila ba, sai ta tsagaita wuta a Gaza

0
112

Saudiyya ta shaida wa Amurka matsayinta na cewa ba za ta ƙulla hulɗar diflomasiyya da Isra’ila ba, matuƙar ba a amince da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta a kan dokokin 1967 ba, da kuma sanya Gabashin Birnin Kudus, a matsayin babban birninta, kuma har sai Isra’ila ta dakatar da kai wa kan Gaza da aka yi wa ƙawanya hare-hare, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya a wata sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza — Ƙungiyar Fursunonin Falasɗinu

A ranar Talata, mai magana da yawun Fadar White House John Kirby ya ce gwamnatin Biden ta sami martani mai kyau cewa Saudiyya da Isra’ila a shirye suke su ci gaba da tattaunawar daidaitawa.

Ma’aikatar ta ce Masarautar ta fitar da sanarwar ne domin tabbatar da tsayuwarta tsayin daka ga Washington kan batun Falasɗinu bisa la’akari da kalaman da ake dangantawa da Kirby.

Leave a Reply