Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan jihar Yobe Hon Mai Mala Buni CON, ya ayyana ranar Laraba 7 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar, domin gudanar da addu’o’in kwana uku ga Marigayi tsohon Gwamnan jihar Sanata Bukar Abba Ibrahim.
Babban daraktan yaɗa labarai na Gwamnan, Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar, inda ya ce Gwamna Buni ya bayyana hakan a yau Talata, inda ya ce a yi amfani da wannan ranar wajen gudanar da addu’o’i ga tsohon Gwamnan da ya rasu a ƙasar Saudiyya ranar Lahadi.
Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa marigayin addu’ar samun dacewa a Lahira.
KU KUMA KARANTA: Tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya rasu
Za a gudanar da addu’o’in kwana uku ga marigayi tsohon gwamnan da ya rasu kuma aka binne shi a ƙasar mai tsarki a masallacin gidan gwamnati dake Damaturu.
Gwamnatin jihar Yobe a hukumance ta ɗauki nauyin jana’izar da ta’aziyyar marigayi gwamnan.
Gwamna Buni, tare da jami’an gwamnati da iyalan marigayi gwamnan, suna ta samun ta’aziyya daga ciki da wajen jihar a gidan gwamnati da ke Damaturu.