Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi bayani kan kisan da aka yi wa jami’anta a Borno

0
121

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta na jihar ta Borno ASP Nahum Daso Kenneth ya fitar ranar Asabar da maraice.

Kenneth ya ce ba a kai hari a “Hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiha da ke Maiduguri ba” kuma tana karkashin kulawar jami’an tsaro sannan tana aiki.

Sai dai ya ƙara da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Unguwar ‘Yan sanda da ke “garin Gajiram na ƙaramar hukumar Nganzai” ranar 2 ga watan Fabrairu da tsakar dare lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu dakarunsu.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a Bauchi sun bankaɗo bindigogin AK-47 da miliyan 4.5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane

“Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda huɗu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare unguwar ‘yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar.

Borno na ci gaba da fuskantar hare-hare daga mayakan Boko Haram da na ISWAP waɗanda suka kwashe shekaru da dama suna addabar jihar.

Mayakan sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu, baya ga sace mutane ciki har da ɗalibai.

Leave a Reply