Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza — Ƙungiyar Fursunonin Falasɗinu

0
192

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Falasɗinu ta zargi sojojin Isra’ila da kashe Falasɗinawa 30 a Gaza.

“An gano gawarwakin mutum 30 da aka ɗaure wa hannu da kuma rufe musu idanu a cikin wata makaranta a Beit Lahia da ke arewacin Gaza,” in ji ƙungiyar fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Ya ce Falasɗinawan da suka mutu sojojin Isra’ila ne suka tsare su kafin mutuwarsu.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya za ta ci gaba da fallasa farfagandar Isra’ila – Altun

“A bayyane yake cewa sojojin mamaya sun aiwatar da hukuncin kisa a kan waɗannan mutane,” in ji ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ce hukumomin Isra’ila sun ƙi bayar da bayanai game da makomar Falasɗinawa da sojojin Isra’ila ke riƙe da su a Gaza.

Leave a Reply