Mali da Burkina Faso sun miƙa wa ECOWAS wasikar ficewarsu

0
132

Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun miƙa wa ƙungiyar ECOWAS takardar buƙatar ficewarsu a hukumance. Ana kyautata zaton Nijar ta bi bayansu kowanne lokaci daga yanzu.

A Lahadin da ta gabata ne gwamnatocin ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka sanar da ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS, bisa zargin ƙungiyar da yi musu barazana.

Sai dai tun a wancan lokaci ECOWAS ta bayyana cewa ta na dakon wasikun ƙasashen 3 a hukumance kan buƙatar ficewa daga ƙungiyar.

A cewar ECOWAS yanzu haka ta na aiki tukuru wajen samar da maslaha a ƙasashen 3 waɗanda dukkaninsu ke ƙarƙashin mulkin soji.

Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta aikewa da AFP kwafin wasikar ficewar yayinda Burkina Faso ta shaidawa kamfanin dillancin labaran aikewa da ta ta wasikar.

KU KUMA KARANTA: Sharuɗɗan da ƙasa za ta cika kafin ficewa daga ECOWAS

Babu dai cikakken bayani daga Nijar, sai dai wasikun ƙasashen qbiyu sun fayyace dalili iri guda a matsayin hujjar da ta tunzura su ficewa daga ƙungiyar.

Ƙarƙashin dokokin ECOWAS dai ana buƙatar aƙalla shekara guda wajen aiwatar da wasu shirye-shirye ga duk ƙasar da ke son ficewa daga cikin ƙungiyar.

Ƙasashen na Mali da Burkina Faso da kuma Nijar na matsayin mambobin da aka kafa ƙungiyar ta ECOWAS da su tun a shekarar 1975 sai dai a baya-bayan nan suna fuskantar takun saƙa bayan juyin mulkin da Soji a ƙasashen wanda ya kai ga kakaɓa musu takunkumai.

Leave a Reply