An yanke wa tsohon Firaiministan Pakistan, Imran Khan, hukuncin zaman gidan yari na shekara 10

Wata kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon Firaiministan ƙasar hukuncin zaman gidan yari na shekara goma a gidan yari, bayan samunsa da laifin bayyana sirrikan ƙasa.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne tare da ɗaya daga cikin mataimakansa Shah Mahmood Qureshi, wanda a baya ministan harkokin wajen ƙasar ne.

Hukuncin da aka yanke a ranar Talata babban ƙalubale ne ga Khan, wanda tsohon ɗan wasan kurket ne wanda aka hamɓarar da gwamnatinsa bayan wata ƙuri’ar yanke ƙauna da aka yi a majalisa a Afrilun 2022.

A yanzu haka dama Mista Khan yana zaman gidan yarin shekara uku kan wani laifi da ya shafi cin hanci.

Mai magana da yawun Jam’iyyar Tehreek-i-Insaf wadda ita ce jam’iyyar da Khan yake a ciki ya bayyana cewa kotun ta sanar da hukuncin da ta yanke ne a wani gidan yari da ke garin Rawalpindi.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya

Hukumomin sun ce Khan da mataimakinsa waɗanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na shekara goma na da damar ɗaukaka ƙara.

Wannan hukuncin na zuwa ne gabannin zaɓen yan majalisa wanda za a gudanar 8 ga watan Fabrairu – wanda zaɓe ne da aka hana Khan tsayawa takara saboda kama shi da laifi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *