Turkiyya za ta ci gaba da fallasa farfagandar Isra’ila – Altun

0
105

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya sha alwashin cewa Turkiyya za ta ci gaba da tona asirin baƙar farfaganda da dabarun watsa labaran ƙarya da Isra’ila ke amfani da su a yaƙin da take yi da al’ummar Falasɗinu na cewa ta daina kisan kiyashi da bala’in da take assasawa a Gaza.

Da yake magana a wani taron tantancewa da hangen nesa na 2023-2024 a ranar Talata, Altun ya ce “komai irin dabarun da masu kisan gilla suke amfani da su wajen ɓoye munanan ayyukansu, za mu jawo hankalin duniya don su ga abin da suke aikatawa a sarari.”

Ya kuma bayar da bayanai game da ayyukan da hukumar sadarwa ta gudanar a shekarar da ta gabata tare da bayyana manufofinta na tsawon lokaci mai zuwa.

Da yake bayyana cewa suna ba da muhimmanci ta musamman wajen kare jama’a daga illolin da ke tattare da hanyoyin sadarwa na zamani, Altun ya ce: “Babu wanda yake maƙiyinmu, amma muna yaƙin neman gaskiya. Kowannenmu yana fafutukar ganin ƙarni na Turkiyya ya kasance ‘Ƙarni na Sadarwa’.”

KU KUMA KARANTA: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya gana da Haniyeh, jagoran siyasa na Hamas, kan tsagaita wuta a Gaza

Altun ya yi nuni da cewa, ƙwararrun ma’aikatan ma’aikatar sadarwa a cibiyar tsakiya da kuma ofisoshin shiyya-shiyya na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa an ji muryar Turkiyya a fage na ƙasa da ƙasa, wajen assasa muhimman tattaunawa a duniya.

“Muna isar da ƙimarmu da tarihinmu mai albarka da nasarorinmu da matsayinmu na siyasa da hanyoyin magance matsalolin duniya da kuma hangen nesanmu na ƙarni na Turkiyya ga duniya tare da haɗakar dabarun sadarwa,” in ji Altun.

Leave a Reply