No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani tsohon soja mai shekaru 72 mai ritaya mai suna Francis Dooga, ya kashe kansa a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Ana zargin marigayin ya rataye kansa ne a kan wata bishiya a gidansa da ke daura da cocin St. Joseph Catholic Church a Iniongun, a unguwar Makurdi da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, 2024.

Wani makwabcin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Dooga wanda aka fi sani da ‘tsohon soja’ ya ɗauki wannan mummunan mataki ne a yayin da ‘yan uwa ba sa gida.

Wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa tun da farko marigayi mai ritaya ya koka da halin ƙunci.

KU KUMA KARANTA: Wani matashi a Kano ya rataye kansa

 An kuma tattaro cewa marigayin ya koka da cewa ɗaya daga cikin ‘ya’yansa yana zare kuɗin fanshonsa da zarar an biya shi.

Ya kuma koka akan rashin samun kuɗaɗen fansho da yawa daga hukumar fansho.

“Kafin ya kashe kansa, mutumin ya kasance yana korafin kuɗin sa na tsaro (SDA) da gwamnatin tarayya ta ba hedikwatar tsaro, wanda kuma aka sake shi ga hukumar fansho ta sojoji.” Inji wani mazaunin garin.

“Ya ce ana biyansu kuɗaɗen fansho ne kaɗan a maimakon a riƙa biyansa kuɗin da yawa a kowane wata, wanda hakan ya haifar masa da tsananin talauci kuma ‘yan uwansa suka yi watsi da shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...