Wani abin fashewa ya halaka yara almajirai a jihar Borno

Daga Ibraheem El-Tafseer

Bayanai na ci gaba da fitowa kan wata fashewa da ta janyo mutuwar wasu yara shida (almajirai) a ƙaramar hukumar Gubio, da ke jihar Borno.

‘Yan sanda da jami’an yankin sun ce fashewar ta faru ne a wani gini da ke makarantar Islamiyya a ranar Asabar.

ASP Nahun Daso, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ta Borno ya shaida wa BBC cewa an tara wasu kayayyakin gwan-gwan da aka yi rashin sa’a wasu matasa da suka je wajen suka taru, a nan ne kuma aka samu abubuwan fashewa da suka tashi.

Rahotanni sun ce yaran kan tara ƙarafa da kuma sayar wa al’ummar yankin.

Duk da haramcin da aka yi kan sana’ar gwan-gwan, har yanzu ana cinikin lalatattun ƙarafa a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu tayar da ƙayar baya.

KU KUMA KARANTA: Mutane biyu sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon fashewar bam a jihar Borno

ASP Nahun ya ce suna wayar da kan mutane game da “na’urorin fashewa” tare da hana saye da sayar da kayan gwan-gwan.

Ya kuma ƙara da cewa rundunarsu za ta yi bincike a kan lamarin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *