No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Usman Ododo ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, bayan nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar cikin watan Nuwamba shekarar da ta gabata.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a Lokoja babban birnin jihar ranar Asabar da rana, inda aka rantsar da shi tare da mataimakinsa, Salifu Joel Oyibo.

Mista Ododo wanda ɗan jam’iyyar APC ne zai maye gurbin Yahaya Bello wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, da gwamnan jihar Yahaya Bello da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, na daga cikin mutanen da suka halarci bikin rantsuwar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...