Mummunan hatsarin Mota ya ci rayukan mutane 18 a hanyar Kano zuwa Kaduna

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 18 tare da jikkata huɗu a ƙauyen Tashar Yari da ke kan babban titin Kaduna zuwa Kano.

Babban kwamandan hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta ƙasa mai lura da shiyyar Kaduna, Kabir Y Nadabo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar da maraicen ranar Lahadi.

Ya ce haɗarin wanda ya rutsa da motar bas ɗauke da fasinjoji aƙalla 20, ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na safiyar ranar Lahadin.

Kabir Y Nadabo ya ce gudun wuce-ƙa’ida ne ya haifar da mummunan hatsarin, inda motar ta faɗa cikin rami.

Babban kwamandan ya ce tuni aka kai mutum huɗun da suka jikkata zuwa babban Asibitin Maƙarfi, domin ba su kulawar gaggawa, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibitin koyarwa na Shika da ke Zariya.

KU KUMA KARANTA: Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Hatsarin mota dai ya kasance ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa mutuwar ‘yan Najeriya da dama a kowace shekara.

Lamarin da masharhanta ke dangantawa da gudun wuce ƙa’ida daga ɓangaren direbobi, da kuma rashin kyawun titunan ƙasar, da ake ɗora alhakinsa kan mahukunta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *