Daga Ibraheem El-Tafseer
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya zama dole kowa ya amince da ‘haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasarsu.
Mista Guterres ya bayyana haka ne a taron ƙungiyar ƙasashen ‘yan ba ruwanmu da aka yi a Kampala babban birnin Uganda.
Ya ce duk wani ƙin amincewa da samar da ƙasashe biyu zai tsawaita rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas.
A ranar Alhamis da ta gabata ne firaministan Israi’la Benyamin Netanyahu ya fito fili ya ƙi amincewa da kafa da ƙasar Falasɗinawa.