An rantsar da shugaban ƙasar Kwango a wa’adi na biyu

0
113

Daga Ibraheem El-Tafseer

A Jamhuriyar Demokurraɗiyyar Congo, a jiya Asabar ne aka rantsar da Félix Tshisekedi, a wani wa’adi na biyu yayin wani biki mai ƙayatarwa a filin wasa na Shahidai dake babban birnin Kinshasa.

Félix Tshiseked ya yi amfani da wannan dama tare da yin ƙira ga ‘yan adawa cewa: “Kuna da matsayin ku a harkokin mulkin ƙasarmu. Ya bayyana cewa ya na da niyar ganawa da su.

KU KUMA KARANTA: An rantsar da mambobin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijar

Yayin wannan jawabin ya isar da godiya ta musamman ga shugabannin ƙasashen da suka halarci bikin rantsar da shi a yau asabar. A ƙarshen bikin rantsar da Félix Tshiseked an gudanar da faretin soji. Bikin ya gudana ne a ƙarkashin kulawar jami’an tsaro da dama.

Leave a Reply