No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar Alhamis ɗin nan ne shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tawagar da ta ƙunshi shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kano a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Jagoran tawagar akwai Shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, wanda ya isa fadar Villa tare da tawagar mataimakinsa daya taba zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan jihar, Nasir Gawuna.

Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin amincewa da babban abokin hamayyar Gawuna, Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe sun gana da shugaban majalisar jihar

A ranar 12 ga watan Janairu ne kotun koli ta mayar da Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano, inda ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ba a bayyana ajandar taron na ranar Alhamis ba kuma waɗanda suka halarci taron ba su yi magana da manema labarai na fadar gwamnati ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...