Mutane biyu sun mutu, 77 sun jikkata a fashewar da ta faru a Ibadan

0
135

Gwamnan jihar Oyo, a kudancin Najeriya, Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu mutane 77 suka jikkata a wata fashewar da ta faru a ranar Talata da yamma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da duka waɗanda suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibiti.

Makinde ya ƙara da cewa kuma su samar da matsuganai na wucin- gadi ga mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon al’amarin.

Gwamnan wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru a Bodija da ke Ibadan babban birnin jihar ya ce, bayanan farko daga jami’an tsaro sun bayyana abun da ya janyo fashewar.

KU KUMA KARANTA: Fashewar rumbun ajiyar mai a jamhuriyar Benin ta kashe mutane 34

Inda ya ƙara da cewa wasu masu aikin haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne da ke zaune a wani gida a wurin suka ajiye abubuwa masu fashewa, kuma su ne suka haddasa fashewar.

Hotunan lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta sun nuna yadda fashewar ta shafi gidaje da motoci da kuma nisan wurin da fashewar ta shafa.

Hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA tace an tura ma’aitakai kai ɗauki da jami’an tsaro, jami’an kashe gobara, jami’an hukumar civil defence da sauransu, domin ayyukan ceto a wurin da lamarin ya auku.

Leave a Reply