Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 60 a cikin dare ɗaya

0
112

Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa 60 a a cikin dare guda a Gaza a sakamakon hare-haren da take ci gaba da kaiwa, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa akwai gomman mutane waɗanda aka raunata a sakamakon munanan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa na atilare a cikin Gaza.

Hare-haren sun faɗa a cikin biranen Khan Younis da Rafah duka waɗanda suke kudanci, da kuma wasu wurare da ke cikin Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar.

Leave a Reply