Namibia ta caccaki Jamus kan goyon bayan Isra’ila ‘mai kisan kare-dangi’

0
129

Namibia ta soki matakin da Jamus ta ɗauka na goyon bayan “Isra’ila game da kisan kare-dangin da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza.”

Shugaban Namibia Hage Geingob ya ce sukar da Jamus ta yi wa Afirka ta Kudu saboda gurfanar da Isra’ila a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a kan kisan kare-dangin da take yi a Gaza ya girgiza kasarsa.

Matakin da Afirka ta Kudu ta ɗauka na kai Isra’ila ƙara a kotun ICJ ya ja hankalin duniya inda ake ta yabonta kuma ake kallonsa a matsayin wani gagarumin tarihi.

Sai dai wasu ƙasashen yammacin duniya ciki har da Jamus sun soki matakin. Kazalika Isra’ila ta musanta cewa tana aikata kisan kare-dangi a Gaza.

Jamus ba ta da kimar da za ta kare gwamnatin Isra’ila bisa kisan kare-dangi da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza da yankin Falasɗinu da aka mamaye, in ji Namibia.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kai hari a ofishin ƙungiyar Palestinian Red Crescent

”A ƙasar Namibia, Jamus ta gudanar da kisan kare-dangi na farko a ƙarni na 20 daga shekarar 1904-1908, inda dubban ‘yan ƙasar Namibia da ba su ji ba, ba su gani ba suka mutu cikin wulaƙanci,” kamar yadda Fadar shugaban ƙasar Namibia ta bayyana a wata sanarwa ranar Asabar da maraice.

Shugaba Geingob ya yi ƙira ga Jamus ta “sake nazari kan wannan mataki da ta ɗauka da bai dace ba inda ta kasance mai goyon bayan kisan kare-dangi da Isra’ila take yi”.

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 23, 000 tun ranar 7 ga watan Oktoba da ta kaddamar da hare-hare a Gaza. Kazalika sama da kashi 85 na al’ummar yankin su miliyan 2.3 sun rabu da matsugunansu.

Leave a Reply