Gwamnatin jihar Yobe ta rarraba kayan aikin gona don inganta noma a jihar

0
137

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA) tare da haɗin gwiwar shirin bunƙasa noma (ADP) sun ƙaddamar da rabon kayayyakin noma a ƙananan hukumomin Potiskum da Nangere domin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

A yayin ƙaddamar da rabon, babban sakataren hukumar SEMA, Dakta Mohammed Goje, ya jaddada cewa, samar da injinan na da nufin inganta ayyukan noma, samar da hanyoyin samun kuɗin shiga, da kuma ba da gudummawa ga ci gaban al’umma baki ɗaya.

Kayan da aka raba ya amfanar da mutane sama da 400 da suka haɗa da injinan sussuka guda goma da injinan haƙar mai guda takwas.

Dakta Goje ya bayyana muhimmancin waɗannan na’urori wajen ƙarfafawa manoman gida ƙarfi da bunƙasar tattalin arziƙi.

A halin da ake ciki, Manajan aikin na shirin bunƙasa aikin gona (ADP) ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kayayyakin da aka raba yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa ADP za ta sanya ido kan yadda ake amfani da su domin hana sayar da injinan ba tare da izini ba.

Da suke miƙa godiyarsu, shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, da waɗanda suka amfana sun miƙa godiyarsu ga Gwamna Mai Mala Buni, SEMA, ADP, UNDP, da jama’ar ƙasar Japan bisa tallafin da ba a taɓa samu ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya amince da biyan naira miliyan 708 ga ma’aikata 461 da suka yi ritaya

Duk da haka, sun bayyana kyakkyawan fata cewa wannan ƙoƙarin zai haifar da fa’ida ta gaske ga ci gaban aikin gona na al’umma.

Leave a Reply