No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata mata a Ostiraliya ta yi sa’a ta kasance a raye bayan da wani maciji mai tsananin dafi ya sare ta a lokacin da take barci a gadonta.

Matar mai shekaru 20 da ba a bayyana sunanta ba an saka ta a jirgin sama zuwa Asibiti sakamakon harin da macijin da ake ƙira ‘Eastern Brown’, mafi dafi na biyu a duniya ya kai mata a gidanta mai nisa da ke yankin Western Downs a kudu maso gabashin Queensland.

Macijin ya ciji matar ne a hannu da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Juma’a 12 ga watan Janairu. Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan’uwanta sun yi mata magani tun farko kafin jami’an lafiya su iso.

KU KUMA KARANTA: Maganin dafin cizon Maciji da na guba

Bayan da aka yi amfani da maganin kashe dafin, sai aka garzaya da matar zuwa Asibitin Toowoomba cikin kwanciyar hankali ta jirgin sama mai saukar ungulu na RACQ LifeFlight.

Budurwar ta yi nasarar ɗaukar hoton macijin wanda ya kutsa kai ya fito daga ƙarƙashin bargon ta.

Jaridar 7News a Ostiraliya ta ba da rahoton cewa tana nan cikin kwanciyar hankali.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...