Saƙon Gwamnan Kano Abba Kabir Ga Nasiru Yusuf Gawuna

0
130

Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ɗan takarar gwamnan kano a jam’iyyar APC Nasiru Yusuf gawuna, yazo su haɗa kai domin ciyar da kano gaba.

Gwamnan ya buƙaci hakan ne, a yayin da yake jawabi ga manema labarai, jim kaɗan bayan futowa daga kotun ƙoli.

Abba yace, hukuncin kotun ƙolin ya kawo ƙarshen taƙaddamar da akeyi akan zaɓen daya gudana a ranar 18 ga watan Maris din shekarar data gabata.

KU KUMA KARANTA: Kotun ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano

Haka kuma gaskiya tayi halinta, duba da yadda kotun ƙoli ta tabbatar wa da Al’ummar kano abin da suka zaɓa.

Domin haka Abba yace ya kamata Gawuna yazo su haɗa kai, domin su kai kano matakin da zata zama abin kwaikwayo, a tsakanin ƙasashen duniya.

A ƙarshe zaɓaɓɓen gwamnan na kano yace, kofa a buɗe take ga dukkan ɓangaren ‘yan adawa domin suzo a ciyar da kano gaba, tunda dukkan su fatan da suke yi wa kano kenan.

Leave a Reply